GABATARWA
Wannan littafi, ‘Magana Jari Ce, 2’, yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin zabo shi kuwa ya rubuta wadan- nan littattafai shi ne ya shiga wata gasa ta rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafınsa na farko ‘Ruwan Bagaja’. An haifi Alhaji Dr. Abubakar Iman, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 191 I a cikin garin kagara sa’an nan tana cikın lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta ‘Ruwan Bagaja’. Ganin kwazonsa wajen f‹aga labari mai ma’ana ya sa Dr. R.M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya. Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu littattafan. A can ya rubuta ‘Karamin Sani kukumi’ cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko ta Arewa. Shi ne ma ya rada mata suna ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’ aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.
Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin ‘Yakin Duniya Na Biyu’ watau ‘Yakin Hitila’ da ya ba suna 'Tafıya Mabudin Ilmi’. Wannan littafi ya ba da la- barin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa ta Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943.
Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne ‘Tarihin Annabi da na Halifofi’ wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin nan yana shugaban Hukumar daukar Ma’aikata ta Nijeriya ta Arewa.
Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nadawa Kwamishinan Jin Kararakin Jama’a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana kiranta Arewa ta Tsakiya. Ya rasu yana da shekara 70 a duniya ranar Juma’a 19 ga watan Yuni, 1981.
Alhaji Abubakar Imam ya rika cewa wannan aiki da ya yi, na talifin ‘Magana Jari Ce’ ya yi masa amfani ainun. Ya kan ce wan- nan aiki shi ne ya ba shi damar zama tare da mashahurin Baturen nan na talifin Hausa, Dr. R.M. East, O.B.E. Ya ce daga gare shi ne ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi.
Abin mamaki, shi kuma wannan Bature, Dr. East O.B.E., a wajen ‘Mukaddamar’ da ya yi da Turanci tun farkon buga ‘Maga- na Jari Ce’, ga abin da ya ce: ’Muna godiya ga En’e ta Katsina, saboda taimakonsu, da hangen nesa da suka yi, har suka yarda, Suka bamu aron malam Abubakar lmam. Suka yarda, ya bar aikinsa, na koyad da Turanci a Midil ta Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadan- nan littattafaı a cikin harshensa.
lyakar abin da mu ma‘aikatan wannan ofis muka yi, na game da talifin wadannan littattafai, shi ne aiki irin na ofis, na shirye al’amuran, yadda suka kai har aka buga su. Ban da wannan sai kuma taimakonsa da muka yi na tattara masa littattafai iri iri, don ko zai kwaikwayi wani samfur. Sai fa kuma wajen shiryawa bayan da ya rubuta.
Kai, in dai har muna da wani abin da za mu yi kirari mun yi, game da talifin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu kawai, shine yadda muka yi har muka binciko wannan malamin
1982 N.N.P.C
MAGANA JARICE
An yi wadansu samari su uku a wani gari wai shi Kona, guda ana kiransa Halilu Wayo, guda Abdu Lura, qaramin kuwa Nahi’u Hankali. Ba banza ba aka lakaba musu wadannan sunannakin, sai don ko wanne halinsa ya dace da a kira shi hakanan.
Suna nan sai ran nan Halilu Wayo ya ce, “Ya kamata mu shiga duniya, mu gwada wadannan baiwa da Allah ya yi mana. Mu ga wanda ya fi, don saura su sakam masa. Amma yanzu ina amfanin muna zaune kurum, kullum sai gardama ta fatar baki?”
Saura suka ce, “Halilu, ai ko gaskiyarka. Da ma an ce maza dangin gujiya ne, sai an fasa a kan san bidi.” Suka shirya, suka dunguma zuwa Bila.
Da suka isa suka nemi su ga Sarki, aka yi musu iso. Suka tafi, suka fadi suka yi gaisuwa. Dogarawa suka amsa, Sarkin Zagi ya tambaye su sunayensu da sana’arsu, da inda suka fito da kuma inda za su. Suka fadi sunayensu dai dai, suka gaya masa kuma sun fito daga Kona ne, za su yawon duniya, don ko Allah ya sa su sami inda za su raba gardamar da ke tsakaninsu.
Sarki ya yi dariya da ya ji sunayensu, sa’an nan ya dube su, ya ce, “Wace gardama ta rabo ku da gida?”
Halilu ya ce, “Ni da Allah ya ba wayo, tsammani na ke duk ba abin da ya fi wayo amfani cikin zaman duniya. Wannan kuwa Abdu tsammani ya ke ba abin da ya fi lura amfani ga mutum. Dan saurayin nan kuwa Nahi’u shi cewa ya ke ba a gama hankali da kome. Saboda haka muka fito dai, mu sami inda za mu raba wannan gardama mu huta.”
Sarki ya ce, “I, ai ko lalle wannan gardama ta isa a rabo da gida, a shiga duniya neman inda za a raba ta.”
To, Sarkin nan kuwa na kiwon balbelu kamar dari. Ka san yadda balbelu su ke, duk kamarsu daya ce, amma duk da haka a cikin balbelun nan akwai wata wadda Sarki ya ke so. Ba don kome ba kuwa, sai don ita ta fi amincewa da mutane. Kullum da ta ga azahar ta yi an taru wurin fadanci, sai ta rabo da 'yan’uwa ta zo kusa da Sarki, ta tsaya yana wasa da ita. Ko da ya ke an saba da ganinta, duk da haka da tashi ta shiga cikin ’yan’uwa ba mai sake fid da ita, don yawansu da kuma kamanninsu da ya ke daya. To, samarin nan sun gama gaya wa Sarki labarinsu ke nan, sai ga balbelan nan ta taso fir, ta sauka bisa kan karagar Sarki.
Da Sarki ya dube ta sai ya ce, “Alhamdulillahi, ga ma inda za ku raba gardamarku, ku huta da wahalar shiga duniya.” Ya kamo balbela ya mika musu, ya ce, “To, kowa ya yi amfani da baiwar da Allah ya yi masa, ya san yadda zai yi ya gane balbelan nan, ko ta shiga cikin dubun balbelu.”
Abdu ya lura da irin siffarta da kyau, tun daga kafafunta har ya zuwa bisa kai. Nahi'u Hankali kuwa bai ko duba ta ba. Ashe kuma sa'ad da Abdu ke lura da irinta, halilu wayo ya kaikaici idanunsu ya zuba mata ruwan goro a fifffike. Da suka jima da ita a hannu, sarki yace su sake ta. Suka sake ta, ta tashi.
Sarki yace, "Na sa fam biyar, da dawaki biyar, da rakuma biyar, da shanu biyar, da bayi biyar, duk wanda ya gane zan bashi. Bayan haka kuma in gina masa gida, in Nada shi sarkin Fadana.
Samarin suka ce, "To munji, mu ko gode, Allah ya kaimu gobe."
Gari na wayewa, balbelu suka taru makil a kofar gidan sarki inda ake basu abinci. Wani bawa mai lura da su ya fita ya ba su abinci. Sarki ya kira samarin, ya ce, "To, ga su can waje, wa zai fara zuwa?" Halilu wayo ya ce shi zai fara. Daren nan kuwa an kwana ana ruwa, saboda haka dan yawun goron da ya zuba ya wanke. Ya nema, bai gane ta ba, ya dawo, ya ce ya kasa, wani ya ta fi.
Sarki ya dubi saura, ya ce, “Wa zai bi?” Sat Abdu Lura ya ce za shi. Ya tashi ya tafi, sai ya iske ashe abubuwan da ya lura da su a jikinta, duk galibinsu ko wacce na da wadannan abubuwa.
Da ya ga ya rude, ya kasa gane ta, sai ya ce, “Kai, wace ce ke son Sarki cikinku?”
Su duka suka amsa, “Ni, ni!” To, ganinka wa zai ce ba ya son ubangijinsa, mai lura da shi kwarai?
Da ya ga dai bai samu abin kamawa ba, sai ya korna, ya ce ya kasa. Sarki ya yi murmushi, ya dubi Nahi’u Hankali, ya ce, “In ta bi daga daga na kurya ka sha kashi.” Sai Nahi’u‘ya tashi ya tafi.
Da isarsa sai ya dube su, ya rike baki wai shi al’ajibi, ya ce, “Kai, ai ko jiya kun kwana kuna waka, amma wannan da ta je wurin Sarki jiya da azahar, ya nuna su da baki, ya ce, “ta fi kowa murya.”
Ko da balbelan nan ta ji an yabe ta, sai ta ce, “Haba samari, don ma ka tarad da ni na tsufa. Da sa’ad da na ke yarinya ce, in na fara waka ai kowa sai kallo.”
Nlahi"u ya ce, “Ai lalle da alama.” Ya sa hannu ya kama ta, ya dauka ya kai wa Sarki. Da Sarki ya gan ta, ya yi mamakin yadda saurayin nan ya gane ta. Ya kawo duk abin da ya ce, ya ba shi, ya kuma nada shi Sarkin Fada. Saura kuma suka shiga cikin fadawan Sarki. Sarkin Fada Nahi’u ya yi musu kyauta daga cikin abin da ya samu. Suka yi aurarraki, suka zauna nan, su da garinsu sai sako ko yaushe wurin iyayensu.
Ran nan da dare suna zaune da Sarki, sai wani maroki ya zo yana ta bunkasa Sarki da kirari, har Sarki ya shiga cikin abin da ya ke fadi, sai Sarkin Fada ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ka ga fa da irin wânnan bunkasarwa ne har na yaudari balbelarka ta tona kanta.” Sai Sarki ya yi sanyi da bin zancen maroka da na makada.
Mutanen Sirika da suka ji akunsu Hazik ya ba da wannan labari, duk sai suka bude hakora suna murmushi na wajensu ya fara da mai dadi.
Da aka natsa, Warizi ya lura da labarin da Hazik ya bayar duk habaici ne ya ke yi masa, shi kuma sai ya kar6a:
Ba Ruwan Arziki Da Mugun Gashi, Wanda Allah Ya Ba Hakuri ya Fi a Zage Shi
Da an yi wani mutum mai arziki, wanda ba a taba samun irinsa ba, sunansa Isa Lamiri. Saboda yawan arzikinsa har duk sa’ad da aka fadi sunansa sai ka ji wani ya amsa da kirari ya ce, “Na- Asabe-karfe-gari.” Babban abin da ya rage masa jin dadin duniya, shi ne ba shi da da, ba shi da jika. Saboda haka ya ke cewa shi ba shi da burin tsibe kudinsa da Allah ya ba shi. Kullum ba abin da ya tsare sai kece raini, ya ci goro, ya busa taba sigari. Mutum ne baduniyi, mai son nishadi, kyauta kuma sai ka ce ruwan sama. ’Yan danginsa kullum su kan nemi su hana masa alherin da ya ke yi, suna cewa, “Isa, kudi ba sa son kazamar bukata.” Shi kuwa ya kan ce musu, “Su kuwa ba su son a samu a kulle.”
Da ya ga ’yan’uwansa sun danne shi haka, sai ran nan ya mila ya sha iska, ya tuna kudin nan dai Allah ne ya ba shi su ba don tanadinsa ba. Ya sa aka tara masa dukan musakai, da makafi, da matsiyatan hasar, ya rarraba musu kudinsa sadaka don Allah, bai rage wa kansa kome ba sai sisi. Ko wannensu ya yi masa addu’a, suka ce yadda ya ji kansu haka Allah ya ji kansa shi kuma, ya saka masa da fiye da abin da ya ba su. Suka watse. Duk gari aka dauki labarinsa. ’Yan’uwa suka yi kamar su kashe kansu don haushi. Da su burinsu, tun da ba shi da da, ba shi da jika, in ya mutu su kwashe kudin.
To, duk wannan abu kuwa ya auku daya ga watan Rabi’ul Awwal ne, watau watan Mauludi. Goma ga watan nan bai cika ba, sai da Isa ya komo abin da zai ci ma sai makwabta sun ba shi. ’Yan uwansa suka yi ta yi masa dariya, suna cewa, “Ai mun gaya maka kudi ba su son kazamar bukata. Ga shi nan yau kwana goma kadai da rabuwa da dukiya, har ka soma bara. Allah ya kara.”
Lamiri ya kama hannunsa za su fita, sai ya dubi Buzaye, ya ce, “Mhm. Kai! Ga kudi a fili, wauta ta sa ku barsu su wuce.” Duk aka fashe da dariya. Aka watse.
Isa Lamiri ya kai shi gida, ya yi ta rarrashinsa yana cewa, “Wallahi kada ka biye wa mafarki, ya sa a daure ka ba ka ci ba, ba ka sha ba. Ko da ka zo nan zaurena da alamar barci-barci ka zo, har kana yi kana tsayawa, sa’ad da ka ke yi mini aski. Shin, in ma ba mafar ki ba, ka taba ganin an bugi mutum ya zama kudi? Lura fa cikin hankalinka.” Ya yi ta kawo masa misalai dai, har ya yarda abin nan dai mafarki ne ya tashi juyad da hankalinsa.
Da Isa ya ga ya ciwo kansa, ya raka shi gida ya dawo. Ko yaushe ya zo ya yi masa aski sai ya tuna masa da wautar da ya yi, su yi ta dariya.
Bayan kamar kwanan wata matar Isa ta yi ciki. Watan nan bai dawo ba sai da ta haifi da namiji. Bai manta da abin da aka gaya masa ba, ya sa masa suna Sa’idu. Aka yi biki da shagali mai yawa.
Dan wanzam kuwa duk inda ya kewaya gari sai mutane su yi ta yi masa ba’a, suna cewa “ Dan wanzam mai Buzaye!”
Mutanen Sirika da suka ji wannan labari sai suka kura wa Waziri Aku ido suna mamaki. Sarkin Sirika. ya dubi Sarki Abdurrahman, ya kada kai. Hazik zai fara wani, Sarkin Sirika ya ce, “Sai mu tafi mu yi la’asar, sai gobe kuma a ci gaba. Abin da a ke yi don nishadi ya zama kamar cin kwan makauniya?”
Alkalai suka yi shawarar darajar da za su ba kowane labari. Da suka gama hankalinsu suka ce, Labarin Hazik talatin, Waziri hamsin.” Mutane suka watse. Sarkin Sirika ya ce wa alkalai, “Ya kamata a rika shari’ar gaskiya dai.”
Sa’an nan alkalan kuma suka ce wa Hazik da Waziri, “Labari kadai a ke so, ban da habaici. Ku kun sani da kayan Sarki Abdurrahaman da na Sarkin Sirika duk daya ne.”
Waziri ya ce, “Hakanan ne. Hazik ne da ma kuruciya ta tashi dibarsa, amma ba kome.”
Da aka isa gida Sarkin Sirika ya kira Hazik, ya ce, “Labarin da ka yi yana da dadi, sai ka yi kokari kuma yau, ka tuna da wanda ya fi shi. Don an ba shi hamsin, ka san wannan ba kome ba ne. Sai mun yi kwana wajen goma sha biyu nan ana labari, tun yana maşu dadi har su kare a bar maka fage.”
Hazik ya ce, “ Don ban san irin kamun ludayinsa ba ne da ma.
Gobe ma gamu.”
Can zuwa magariba sai Waziri ya aiko Hazik ya tafi su ci abinci tare. Aka dauke shi aka kai, aka kawo musu abinci iri iri suka yi ta ci, wadansu ma Hazik bai taba ko jin sunansu ba.
Da suka gama Waziri ya sa aka kawo goro aka bara musu, ya cika bakinsa, ya mikawa Hazik bari. Hazirk ya ce ai shi bai taba cin goro ba, yaya zai yi ya tauna shi ma? Waziri ya yi murmushi, ya sa aka mai da Hazik gida, ya tafi yana ta mamakin wannan irin daula da Waziri Aku ke ci haka.
Da gari ya waye, azahar ta yi kuma aka sake taruwa, Hazik ya fara:
Labarin Kalala Da Kalalatu
Akwai wani mutum wai shi Kalala, yana da matarsa wadda a ke kira Kalalatu. Kalala Allah ya yi shi wani irin mutumin da ne, ba abin da ya fi da qi illa a yi masa abinci ya ci shi kadai. Da suna ci tare da wani makwabcinsa, sai makwabcin ya zama wani iri ne mai mita. Ya kan rika cewa Kalalatu ba ta iya miya ba, wai kullum miyarta daga ta cika gishiri sai ta cika ruwa.
Da Kalala ya ga tsegumin yafa yi yawa sai ya bar kai abincinsa wurin mabwabcin. Ya riqa fita karauka yana nemo baki, yana kawowa gidansa suna ci tare.
To, Kalalatu ba ta kaunar wannan dabi’a ta mijinta, domin bisa ga misali, ran da Kalala ya yanka kaji biyu, iyaka Kalalatu ta sami cinya, domin duk Kalala zai kai wurin bakin da ya jawo ne su cinye. Ta yi, ta yi ta hana shi wannan dabi’a, ya ki hanuwa. Saboda haka sau da yawa in ya ba ta dahuwa sai ta tsame rabi ta cinye, in Kalala ya yi magana ta ce ya kone ne, ko kuwa ta ce ta sauke ta shiga daki dauko kwano, kafin ta fito ta tarar kyanwa ta cinya rabi. Dalilai dai irin wadannan marasa kan gado ga su nan kullum Kalala na ta sha, amma saboda hakurin da Allah ya zuba masa ba ya cewa kome.
Ran nan, ko ina Kalala ya sami kudi sai ya tafi kasuwa ya nemo dakwalen kaji guda biyu ya sayo. Ya yiwo cefane ya kawo gida, ya ce wa Kalalatu ta soye kajin nan gaba daya. Ta tashi, bayan ya fige ya gyara mata, ta sa tukunya ta shiga suya. Abu ga dakwalen kaji, duk kitse yâ cika tukunya, sai wani abu su ke coi, coi, coi, in tana juya su. Duk kuwa kwadayi ya kama ta, da ma ga ta idonta idon nama sai ka ce kura sai yawu ke zuba dalala. Ta sa dan yatsa ta dandana ta ji ko gishiri ya yi daidai, sai ta ji abin dadi ya kamo ta har ga keya, ta ce, “Kai, wadannan kaji yau suna shirin ganin wata irin gajerar suya. Amma dubi duk yawan kajin nan, rabona bai fi cinya ba daga cikinsu. Ka san dai halin mai gidan nan ya miskile ni.”
Ta ci gaba da suya qanshi na jifarta, ta yi kamar ta jure ta kasa, sai ta fara tsame tana ci, wai ta kau da mugun yawu. Kafin su soyu ta kusa cinye rabin kaza. Da ta sauke sai ta je ta gaya wa mijin sun soyu.
Kalala ya ce, “To, sai ki cire cinya guda, taki ke nan. Saura kuwa a ajiye, har in je in samo abokan ci.”
Kalalatu ta ce, “To.” Ta tafi ta cinye ’yar cinyar da aka ce ita ce tata, ta tsuguna tana kallon saura, sai mai ke zuba nash, nash. Ta ruga wajen kofar zaure ta leka ko ta hango mijin tafe da bakin, ba ta ga kowa ba, ta komo wajen kaji ta tura musu ido. Sai ta ce, “Af, ashe ma fikafikai guda biyu sun kone tun dazun, bari in cinye na dayar kuma don su zo daidai, kada mai gida ya gane.” Sai ta kama fikafikai ta fiffizge ta lakwame. Ta sake rugawa bakin zaure ta gani ko mijin na tafe, ba ta ga kowa ba. Ta dawo, ta tsaya bisa kwanon da kaji su ke, ta ce, “Shin mai gidan nan zai zo dai? Ga kaji har sun fara yin sanyi. To, ni Kalalatu, yanzu in ya zo ya tarar wannan kazar duk na fiffige ta, ya tambaye ni, in ce me? Ba abin da yafi sai in cinye ta gaba daya, in ya zo in ce kyanwar gidan nan ta sace ta.” Sai ta tsuguna ta cinye ta sarai, ta kwashi kasussuwa ta kai masai ta zuba.
Ta koma kofar zaure ta hanga, ba ta ga mai gida ba. Da ta ga haka sai ta dawo, ta ce, “A bari ya huce shi ya kawo rabon wani. Bari in karkare cinya guda, kowa ya huta, in ya so in ya dawo kome ta tafasa ta kone.” Sai ta kama kazar guda kuma ta lakwume. Ta nufi randa ta debi ruwa ta kora, ta yi gyatsa, ta ce, “Madalla, kome ta ke zama ta zama.”
Ta zauna ke nan, sai ga mai gida ya shigo. Ya ce wa Kalalatu, “Yi maza ki nika yaji ki barbada musu, kin san yanzu lokacin sanyi ne, ba abin da ya fi yaji amfani. Na manta ne in gaya miki ki nika yaji dazun. Yi hakuri, yau dai kin sha aiki.”
Kalalatu ta ce, “Ai ba kome, ku dakata mini dai kadan.’ Ta shiga daki tana ta shawarwarin abin da za ta ce wa mijin ya faru ga kaji. Tana can cikin daki, sai Kalala ya dauki wuka ya nufi manika yana wasawa kararas, kararas, wai don ta yi kaifi ya sami ta yanka kaji kanana kanana, in an kawo.
Kalala na can na ta fama da washin wuya, sai Kalalatu ta ji ana sallama. Ta yi farat ta fita bakin zaüre wajen mai sallama, ta dube shi ta rike baki, ta ce, “Kai bako, kai ne mai gidan nan ya kirawo, wai ku zo kucï abincï?”•
Bako yace, “I, Allah ya saka muku dâ alheri.”
Kalalatu ta ce, “Kai, tafi can, sakarai' ba ka san abin da a ke ciki ba. Kana tsammani mutum mai hankall ya sa a yi masa abinci ya fita karauka neman abokin ci? In kana kama gabanka ka ruga, tun da wuri ka ruga. Ka ji shi can yana washin wuka, kunnenka guda zai yanke. Kullum haka ya ke yi, motsattse ne.”
Bakon nan, ko da ya saurara ya ji Kalala na washin wuka sai ya dafe qeya ya zura a guje. Kalalatu kuma ta ruga wajen Kalala, ta ce, “Ga irin jaye-jayen naka nân, ba ka san irin mutanen da ka ke jawowa gida ba.”
Kalala ya ce, “E? Mahaukaci ne?”
Kalalatu ta ce, “Mahaukaci mana, ko ba mahaukaci ba ne ai barawo ne, da barawo ko da mahaukaci ai duk tafiyarsu ke nân. Kajin da na barkadawa yaji, ko da ya gan su sai naga ya yi wuf ya fizge, ya shafa a guje da su. Ga shi can ya mika, ya tasarwa kasuwa.”
Kalala ya fusata, ya ce, “Allah wadan dan banza! Mutanen duniya ba wanda ke iya musu. Da ma ya bar mini ko da guda daya, ai da na sami ta kalaci. Dakwalen kajin nan duk ya cinye shi kadai? Bari in leka ko na hango shi, mu raba.” Sai ya ruga wajen zaure ya hanga, sai ga bakon nan can ya tattake da gudu kaca kaca kaca yana korar iska. Kalala ya ce, “Kai abokina! Kai tsaya, don Allah ko guda daya ka ba ni! Wallahi su ke nan, mai dakina ko lasawa ba ta yi ba, ka dauke.” Bako ya yi kamar bai ji ba.
Kalalatu ta ce wa mijin, “Bi shi mana, a guje dai na san ba ya tsere maka. Duk wahalan nan da na sha ta zama a banza, ko lasawa ban yi ba, ai ka san ka dauki alhakina.”
Sai dalala ya runtuma a guje da wukarsa a hannu, ya bi bako yana kira, “Tsaya don Allah, daya kadai na ke so, na bar maka daya!”
Bako tsammani ya ke Kalala na nufin kunnensa daya kadai ya ke so ya yanka. Ya waiwaya sai ya ga ya taso masa da wuka tsirara a hannu. Saboda haka ya kara mai, ya dai yi wa Kalala fintinkau yana ji yana gani.
Da Kalala ya ga abin ba girma, sai ya juyo ya nufo gida da wukarsa a hannu, yana kutawa, yana Allah ya isa. Da matar ta ganshi ya dawo yana zage-zage sai ta tarye shi, ta ce, “Ya ba ka? Ka ga irin abin da na ke gaya maka nan tuni.”
Kalala ya ce, “Ko tarad da shi na yi? Wannan akwai dan banza da gudu! Ga shi kamar tsoho, amma da ya zura sai ganinsa a ke kamar ba ya taka qasa. Bar shi ya je ya ci, ban dai yarda masa ba duniya da lahira. Allah ya isa. Daga yau ko sai yau, ba na sake kiran dan kowa yaci abincina, tunda duniya ta sake. Mts, Allah wa- dai! Talaka dai ba aboki ne ba, ko ka so shi . ran biki kwa bata.”
Mutane da suka ji wannan labari suka fashe da dariya. Da suka yi shiru Waziri ya soma:
Labarin Yusha’u Na-Narimi Dutse-Ba-Ka-Fargaba
Da, an yi wani yaro wanda Allah ya nufa da wata irin zuciya sai ka ce dutse, don rashin fargaba. Saboda ganin haka sai ya rika alfahari, yana cewa shi duk duniyan nan bai ga wani abin da zai bashi tsoro ba har ya kadu. ’Yan’uwansa yara su kan kulla abubuwa da yawa yadda za su sa ya kadu, amma duk a banza. Saboda haka har suka sa masa suna ‘Dutse.’ Da sun gan shi sai su rika yi masa kirari suna cewa, “Yusha’u Na-Narimi, dutse-ba-ka- fargaba.”
Da kakansa ya ji haka, sai ya ce shi lalle sai ya ba shi tsoro har ya kadu. Yusha’u kuwa duk bai san abin da a ke ciki ba. Ran nan da tsakad dare sai ya tafi hira wata unguwa, ya raba dare bai dawo ba. Da kakan nan nasa ya ji haka sai ya tashi, ya sami karare, ya daura wani mutum-mutumi dogo, ya sa masa farar riga, shi kuma ya sa wa kansa fara. Sai ya tashi ja dauki mutum- mutumin nan ya dora bisa kansa, ya tafi hanyar da yaron nan zai biyo, ya maqe.
Can zuwa tsakad dare, duk ba wani mahaluki mai motsi, sai ya ji yaron nan tafe yana waka. Da jinsa sai ya fito daga inda ya ke boye, ya tasam masa haikan. Da Yusha’u ya ga ya nufo shi sai ya ce, “Kai tsololo, in aljani ne kai, lalle Allah bai halicce ka da tsari ba, ga ka tsololo, amma dan kai sai ka ce kodago. Ko kuwa fatalwa ce? In kuwa fatalwa ce, na so in gan ta sa’ad da ta ke da rai. Zotori!”
kakansa dai bai ce uffan ba, ya dai nufo shi har ya taka wa yaron nan kafa. Sai yaron ya tsaya, ya ce, “A’a! Shakiyancin nan na aljannu da fatale har ya kawo gare ni? Kai tsololo, mene ne na taka ni? To, ko da ya ke tsawona bai kai ın mareka ba, ai ka sha kulki!” Sai ya dunkula hannu, ya kaiwa kakan bugu, tim!
Ya sake dagawa zai kara, sai kakan ya yad da karan, ya ce, “Kai, kai, kai, ni ne kakanka Narimi, kada ka buge ni.”
Yaron ya yi murmushi ya ce, “Kaka, me ya sa ka yi mini haka, ga shi har ka sa na buge ka?”
Narimi ya ce, “Mutane na ke ji suna cewa, ai wani abin da za a yi maka har ka kadu, shi ya sa na yi wannan dabara wai ko na sa ka ji tsoro. Ashe dai gaskiyarsu. Gobe kuwa sai na tafi na gaya wa Sarki jaruntakan nan taka.”
Yaro ya ce, "Shin kaka, mene ne tsoro ne? Ni ban san abin da a ke kira hakanan ba. Ashe yanzu nan duniya har akwai abin da zai sa In kadu?” Kakan ya yi murmushi, ya korna gida.
Gari na wayewa sai kakan ya tafi ya gaya wa Sarki, ya ce yana da jika wanda ba abin da za a yi masa ya kadu. In Sarki yana so ya gani, ya kirawo shi ya gwada shi. Fadawa suka ce, “Allah ya ja zamaninka, wannan yaron ai sananne ne a kan rashin tsoro, ai tun da ya ke babu abin da ya taba sa shi ya kadu.”
Sarki ya ce, “To, madalla, gobe, ku zo da shi mu gani. Ai inda ba kasa a ke gardamar kokawa.”
Da gari ya waye kakan ya kira yaro, ya gaya masa abin da suka yi da Sarki; Yaro ya ce, “To, sai mu tafi, in shakka ya ke yi.”
Da aka yi sallar azahar, da yaro da kakansa suka tafi gidan Sarki. Suka tarad da fada ta cika, kowa na fadin albarkacin bakinsa. Suka fadi suka yi gaisuwa. Dogarawa suka ce, “An gaishe ku.”
Sarki ya dube su, ya ce, “Kun taho”
Kakan ya ce, “I, Allah ya ba ka nasara, ga yaron.”
Sarki ya dubi jama’a ya ce, “Kun ga yaron da aka ce bai ta6a kaduwa ba don tsoro. Ina so in gwada shi, amma ku shaida, ln aljannu suka halaka shi, ko kuwa suka zauta shi, kada a zarge ni. Zan sa shi ya kwana cikin dakin gindin tsamiyan nan ta gunki. In ya tashi lafiya gobe, ba a ji ya yi kuwwa ba, ko wata firgita, zan ba shi ’yata aure.”
Da kakan yaron nan ya ji haka sai idonsa suka yi kwal-kwal. Fadawa kuma duk suka dube su, suka yi dariya. Kowa ya san tsamiyan nan akan kwankwamai. Nan ne kuwa fadar Sarkin aljannu. In mutum ya bari magariba ta yi masa, ko kuwa rana ta take yana kusa da wurin, sai wani ba shi ba. Wannan abu ba ko camfi ba ne, an ga haka ba daya ba, ba biyu ba. Saboda yawan aljannu har a ke kiranta “Mutuwa kusa.”
Da kakan yaro ya ji haka sai ya ce, “Ranka ya dade in dai wannan za a gwada shi, ba ya iyawa, kwarinsa bai kai haka ba.”
Yusha’u ya yi wuf ya ce, ‘Me ya sa ka ce haka? Cikin duniyan nan ashe har akwai wani abin da zai sa ni in kadu ma, balle har a ce in yi ihu? Haba, ranka ya dade, ko ba ka san labarina ba ne? Ni ne fa Dutse Na—Narimi ba ka fargaba. Allah ya kai mu magariba.”
Kakansa ya yi, ya yi, ya hana shi, ya tsaya shi sai ya kwana. Narimi ya gaji, ya ce, “Jeka, ai mai rabon shan duka ba ya jin kwabo, sai ya sha.” Suka sallami Sarki, suka tafi gida, duk Narimi ’na zulumin abin, yana cewa, "Lalle baki dai shi ke yanka wuya,”
Magariba na yi sai yaron nan ya dauki ’yar tabarmarsa, ya tafi gindin tsamiyan nan, ya shige dakin ya yi shimfida, ya kunna fitila, ya kwanta, ya bar ta tana ci. Aka zo aka gayawa Sarki. Sai ya sa wadansu malamai su hudu, suka sami wani wuri can nesa da gindin tsamiyar, suka buya. Suka tsayâ daidai da inda za su iya hanğen duhun yaron nan cikin daki; don kada ya fito.
Yana nan kwance sai ya ga wani aljanni ya keto bangon dakin ya fito, duk tsawonsa bai fi kamu guda ba. Amma kansa, duk inda tulu ya kai da girma ya fi hakanan. Da fitowarsa sai ya zauna gindin fitila tare da yaron, ya yi masa kuri da ido. Sai Yusha’u ya ce masa, “Me ka ba ni ajiya ne. har ka dame ni da kallo haka? Ko kuwa kana da wani da ne kamata wanda ya bace?” Aljannin nan dai bai ce masa uffan ba, sai lashe-lashen bakinsa ya ke yi. Yaro ya ce, “Kurwata kur, ka ci kanka, ka sha bakin ruwa!” Aljanni dai bai ce masa kome ba.
Suna nan zaune, sai ga cinyar mutum ta fado kasa tim, har da jini. Yusha’u ya dubi cinyar, ya ce, “Kai, mai wannan cinya lalle kafin ya mutu an yi kato! Shinkici! Amma irin kattan nan galibi ba su kan yi karfi ba. Bari in jinjina cinyar, in ji in da alamar karfi.” Ya tashi ya ciccibi cinyan nin ya ji ta sakwat, ba nauyi. Sai ya ce, “Allah wadai, yau ga katon kwabo! Ashe duk katancin nan ta gina ne ba ta shiga ba.” Sai ya yar da ita waraf, ya korna kusa da gajeren nan na tsugune. Ya zauna ke nan, kuma sai wata cinyar ta fado kusa da ta fari. Kafin a yi haka kuma sai ga hannuwa sun fado. Yaro dai bai ce kome ba sai dariya ya ke yi musu. Can kuma sai ga gangar jiki ta fado tirim. Ko wace gaba ta like ga ’yar’uwata, sai ga mutum ya tashi ya nufo su, amma ba kai. Yaron nan ya ce, “Kai, wannan huhun ma’ahu ya faye doki! Tsaya mana tukun kanka ya fado sa’an nan ka zo, in hira za mu yi.”
Aljani dai bai ce kome ba, sai ya zo wurin wancan dan gajeren nan da ya fara zuwa, ya danne shi, ya kama hannunsa guda ya kakkarya shi rugu-rugu, ya bar shi nan yana kuka. Ya zabura zai gudu sai ga wadansu aljannu guda biyar sun tsago kasa sun fito. Da ganin abin nan da ya faru, sai suka yi cacukwi da wannan da ya karya dan uwansu, suka ce, “A’a, a, a! Kai Kururrumi, kai ka karye Dandagizge? Wallahi yau in Sarkin Aljannu ya zo, bari ta kai, ko da mutumin nan mai fitala da ke nan aka yi abin, kashinsa ya bushe!”
Sai yaron nan ya ce, “Kai, in kuna shiriritarku ku bar gamawa da ni. Ka ga ’yan nema masu manyan kunnuwa! Kashina ya bushe! Halama ni na kashe shi?”
Kai, in-gajarce muku labari dai, aljannun nan suka yi ta ba shi tsoro iri iri har gari ya waye, amma Yusha’u bai razana ba, balle ya kadu.
Da rana ta fito ya dauki ’yar tabarmasa, ya nufi gidan Sarki, ya ce ya dawo. Mutane za su yi muşun bai kwana ba, sai malaman nan hudu suka shaida ya kwana. Sarki ya rasa abin da ke masa dadi, ga shi ya yi alkawari ba damar warwarewa. Mutane suka yi ta mamakin yaron nan, kakansa kuwa ya yi ta farin ciki da ya kubuta.
Sarki ya tashi, ya shige gida duk rai a bace, ya kira ’yar da uwarta, ya gaya musu wannan al’amari duka. Yarinyan nan ta ga ran iyayenta ya baci, sai ta ce,‘“Kada ku bata rayukanku a banza, na ce ko kaduwa ce ya ce bai ga abin da zai sa shi ya yi ba?”
Uban ya ce, “I, lalle ko gaskiyarsa, duk duniyan nan kuwa babu.”
Yarinya ta ce, “To, na ce ko kun gama naku na manya? Saura kuma mu mu yi kokarimmu na yara, mu gani.”
Uban ya yi dariya ya ce, “Wane kokari gare ku na yara ban da wauta?”
Yarinyar ta ce, “Ina so, in ka yarda, baba, ka je yanzu cikin taro, ka ce ka ba shi ni, amma da sharadi guda, shi ne daga yau har kafin rana wa ta yau, in wani abu ya sa shi ya kadu, baiko ya tashi.”
Uwar ta yi dariya ta ce, “Ka ji wautar tamu ta mata! Wanda ya kwanta dakin gunki bai ji tsoro ba, to, me zai tsorata shi a cikin gidansa?”
Uban ya ce, “Bari in je in fadi, kada mu rage mata hanzari.”
Sai ya korna zaure ya fadawa mutane haka, duk suka shaida. Yusha’u ya yi dariya, ya sallami Sarki ya tafi gida, iyayensa suka yi ta yi masa guda don murna. Yarinyan nan kuwa ta san tun da ya kwana dakin gunki jiya, lalle aljannu ba su bar shi ya runtsa ba, tun da abin ya ke haka kuwa, daren yau lalle in ya fara barci sai Allah. To, lokacin nan kuwa cikin tsakiyar dari ne muku-muku. Saboda haka da asuba sai yarinya ta tashi ta fadawa ubanta, ta sa ya aike aka tado Waziri da Alkali, da manyan malaman gari guda hudu wadanda Sarki ya sa su tsaron nan jiya da dare. Da suka taru, sai yarinyar ta debo ruwa mai sanyi kwarai daga wani sabon tulu, ta ba Sarkin Zagi ya dauka, duk suka dunguma zuwa gidan.
Da suka isa kofar gida, ta ce kada kowa ya yi magana, ko wani babban motsi. Ta sa aka tafi sululu aka tado kakan yaron nan, ya fito waje ya tarad da su, kowa dai ya zuba wa ’yar yarinya ido ya ga abin da za ta yi. Sai ta ce kakan yaron ya shiga gaba ya nuna musu dakin jikansa, amma fa ba a ce in ya je ya ta da shi ba, ko motsi mai karfi ma kada kowa ya yi.
Suka isa, ta tarad da dakin rufe da asabari, ta sa hannu sannu a kan hankali ta cire, sai ga yaro kwance tim, daga shi sai durwar bante, barci ya sa har ya ture dan bargonsa bai sani ba. Sai ta karbi ruwan nan ta shiga cikin dakin sadadaf, sadadaf, ta watsa masa a jiki. Ko da ruwan nan ya zuba masa sai ya kadu, ya yi firgigi ya tashi, ya ce, ‘Wai!” Duk mutanen nan suka yi tafi baki daya, suka bushe da dariya, suka ce, “A’ ya kadu, ya kadu!”
Da Yusha’u ya bude idonsa, ya gane makirci ne aka yi masa, sai kunya ta rufe shi. Don gudun jin kunya bai bari gari ya waye masa ba, sai da ya gudu ya bar garin. Mutane suka yi ta mamakin wannan fasaha ta ’yar yarinya.
Da Sarki ya komo gida ya gaya wa uwar yarinyar abin da ya faru, duk sai suka rungume ta don murna. Da gari ya waye Sarki ya nemi yaro, aka ce ai ya gudu. Sai ya sa mutane su bi shi. Kafin azahar aka komo da shi. Sarki ya nada shi Sarkin Yaki. Aka ba shi katon gida. Sarki ya aura masa ’yam mata biyu daga cikin ’ya’yan bayinsa. Da ma abin da ya tsana ya ba shi ’yar cikinsa, ga shi talaka. Sarki kuma ya yi wa kakan yaron nan kyauta mai yawa don jaruntakar jikansa. Suka yi ta cin duniyarsu a tsanaki. Kullum idan Sarkin Yaki ya tafi fada Sarki ya ce masa, “Yusha’u, Sarkin Yaki, Na-Narimi, dutse ba ka fargaba.” Shi kuma sai ya ce, “Lalle ba na fargaba sai na ruwa, Allah ya ba ka nasara.” Duk sai a yi ta dariya.
Mutane suka ce, “Ba Sarki ne kadai ba, kowa ya ji wannan labari ai lalle ya yi dariya.”
Alkalai suka ce, “Hazik ashirin, Waziri saba’in.”
Sarkin Sirika ya bata fuska, ya ce, “Kaliyâni fin nari wa kali filjannati.”
Ana komawa gida kuma Waziri ya sa aka tafi aka kira Hazik suka sake yin dina tare. Da suka gama ya sa aka dauke shi; aka mai da shi gida. '
Gari na wayewa küma, da aka yi sallar azahar sai aka sake taruwa. Mutane har daga kauyuka suka yi ta zuwa, don sun ji labarin wannun babban taro. Aka sa mutane suka yi tsit, sa’an nan Hazik ya shiga aikinsa.
Marar Gaskiya Ko Cikin Ruwa Ya Yi Ji6i
Wata rana wadansu Filani su bakwai suka tashi daga rugarsu za su yawon sharo. Suna cikin tafiya sai suka kai wani gari, suka ga in sun wuce dare zai yi musu ba su kai gari na gaba ba. Saboda haka suka sami wani katon zaure a gidan Sarkin Fawa, suka sauka. Ashe guda na da kudi, bai gayawa kowa ba cikin ’yan uwan nan. Sai can da dare suna hira, ya dauko kudin nan ya qidaya su sule goma sha biyar, ya mayar ya kulle a warki, ya ce, “Na she im mun je ni sai na samo aure.”
’Yan’uwansa suka ce, “Mun she mu ma ko da ba mu jo da kudi ba, da danshe na she ma samo.”
Can da dare ashe guda duk haushi ya kama shi, don shi bashi da ko anini. Sai ya tashi ya sace kudin nan, ya kai ya binne, ya komo ya kwanta.
Da gari ya waye za su tashi, mai kudin nan ya kwance warki wai ya dauko kudi ya kidaya, kudi suka ce cfauke mu inda ka ajiye. Ya fa tashi da zage-zage, ya ce ’yan’uwansa suka sace don bakin ciki.
Da Sarkin Fawa ya ji zage-zage a zaure, ya fito ya tambaye su. Mai kudin nan ya mai da jawabi duka. Da Sarkin Fawa ya ji haka, ya yi kokari ya sami wanda ya dauka, ya rasa. Sai ya ce wa mai kudin, “Ka yarda, ko kuwa in kai ku ga Alkali?”
Mai kudi ya ce, “A’a? Sai a kai mu ga Alkali, na she kudin nagge guda in yadda shi, ai ba shi yiwuwa.”
Sarkin Fawa ya sa su gaba har Majalisar Alkali. Alkali ya tambayi mai kudin nan, ya bayyana masa yadda aka yi. Da Alkali ya ji haka sai ya ce wa sauran Filani, “Ashe da ma abin ba sacewa kuka yi ba? Don Allah ku ba shi kudinsa, ku tafi abinku. Da ya ke da wasa kuka dauka ai ba ku bari a zo gaban magabata ba.”
Sai duk baki daya suka ce, “Renki shi dade, ai mu ba mu daukar masa kudi ba.”
Alkali ya ce, “Haba, ku kun fiye son wasa, na ce ko kun gwada shi ne ku gani ko ya karaya. To, ya yi raki, ku ba shi abinsa, ku tafi ku ba ni wuri.”
Filani suka tsaya tsakani da Allah su ba su daukar masa kudi ba. Da Alkali .dai ya‘yi wadannan 'yan dabarunsa na mahukunta ya ga abin ya ki, sai ya samo dogwayen sanduna guda shida, ya auna tsawonsu, kowa na kallo, ya yanke su dai dai da juna. Ya dauka ya rarraba musu, ya ce wa Sarkin Dogarai, “Tafi da su gidan wakafi sai gobe. An ce in wasa ku ke yi, ku fadi gaskiya ku tafi, kun ki. To, in ni Alkali ne ba karya ba, na kuwa gaji abin nan, kaka da kakanni, gobe in kun zo a ga sandan barawon nan tafi ta saura da rabin taka. Ku jama’a, duk kun ga tsawonsu daya ko?”
Mutane suka ce, “I, Allah ya gafarta malam.’
Ya dubi Filani, ya ce, “Ku kuma kun gani hakanan ne ko?” Filanin suka ce, “I, Allah shi dade da renki."
Alkali ya ce,
“To, Sarkin Dogarai, tafi da su. Kai kuwa Sarkin Fawa tafi da wannan mai kudin gidanka sai gobe.” Suka tafi. Da dare ya yi tsaka, kowa ya yi barci, sai harawon nan ya rasa abin da ke masa dadi a duniya, ya tabbata gobe Alkali daure shi zai yi in an sami sandansa ya qaru da rabin taka. Saboda haka sai ya gwada rabin taka, ya zaro wukar da ke gindinsa ya yanke, ya ce watau gobe in sandansa ya qaru da rabin taka, sai ya yi daidai da na saura.
Da gari ya waye Alkali ya zo gidan shari’a, sai ya aika Sarkin Fawa ya zo da bakonsa. Sarkin Dogarai kuma ya taso qeyar wadancan, kowa da dogon sandansa a hannu. Da suka taru Alûali ya ce, “To, jama’a, kowa ya matso ya gani.” Da suka matso duk Filani suka zaro ido su ga ikon Allah. Sai ya karbi sandunan ya gwada su, sai ga sandan barawon ya kasa na saura da rabin taka. Alkali ya fashe da dariya ya sa dogarawa su tambaye shi sai ya nuna inda ya boye su.
Da Bafillacen nan ya ji abin ba dama sai ya ce, “ Wayyo Allah, she ma Alkali ya sa a bi ni in kawo.”
Alkali ya ce wa dogarai su kyale shi. Ya sa Sarkin Dogarai ya bi shi inda ya binne, ya tono ya kawo. Aka ba mai kudi abinsa. Alkali ya sa aka yi wa barawon nan bulala shida, aka daure shi wata uku. Saura kuwa ya sallame su, suka korna rugarsu suka ba da labari. Da aka sake shi sai ’yan’uwansa suka yi ta yi masa ba’a, suna kiransa “Dogo mai gajeren sanda.”
Da Hazir ya kai karshen wannan labari sai Waziri ya ce, “Ka taba karanta wani littafi na Larabci da a ke ce masa Bahrul’adab ne?”
Hazik ya ce, “Me ka gani?”
Waziri ya ce, “Wannan labari naka na san can ya ke.” Hazik ya ce, “A’a, ni na qago abina.”
Waziri ya ce, “Kada ka ja wata gardama da ba ka da gaskiya cikinta. Abin da ka sake cikin suna biyu ne ka‹fai. Na farko, ka ce Filani ne, na biyu, ka sa wa mai gidan da suka sauka suna Sarkin Fawa. Ban da wadannan ba abin da ka sake. Ka dai yi kokari da ka hardace da kyau haka.”
Hazik da ya ji ba ya da gaskiya sai ya yi shiru, kada a nemo littafin a buda a gani ya ji kunya.
Da aka yi shiru Waziri ya ce wa Hazik, “Bari in gaya maka akasin labarin da ka bayar.”
Ba Gaskiya Ba ce A Bar Bida Ga Shari’a, Kai Dai A Samo Sa’a
Mutane suka ce, “Wannan lalle ya sami sa’a hakika. Ga shi ya tashi da fam arba’in ris.”
Alâalai suka ee, “Hazik goma, waziri.........” daga nan sai Sarkin Sirika ya yi farat ya katse wa Alkalai magana ya ce “Kai, mu ba mu son irin daraja-darajan nan taku. Ko ba a rubuta ba mu ba mu iya tunawa?” Sai ya tashi, ya karbe allon ya goge rubutun da ke ciki, ya jefar.
Sarki Abdurrahman ko da ya ga haka, sai ya ce me zai yi ba dariya ba. Aka watse. Da aka isa gida Sarkin Sirika ya ce wa Hazik, “Yanzu sai ka saki jikinta, ko nasa sun fi dadi, in an kare sa’ad da za mu koma gida, in aka zo a fadi wanda ya fi, ba na yarda a ce kai ne baya. In dai ba a ce kai ka fi ba, sai dai a ce kuna daidai.”
Hazik ya ce, “Ai don wannan ba kome. Allah dai ya kaimu gobe. Ai da ma masu karin magana sun ce, “Ta safe ta raggo, in rana ta yi sai mu mutanen Sarki.”
Da gari ya waye aka taru, sai Hazik ya kama aiki ya ce, “Af, Allah ya ba ka nasara, tun da na ke ba da labari har yau ban ta6a ba da na 6arayi ba. Ka san ko na yi babbar mantuwa.”
Waziri ya ce, “A'a, tsaya, mu ba mu son labarin 6arayi.”
Hazik ya yi burwaya, ya kada fiffike, ya ce, “Ayya! Don me ka ce ba ku son labarin 6arayi? A cikin labarurrukan nan na duniya har akwai wadanda suka fi na barayi da ’yan fashi sha’awa da mamaki?”
Waziri ya ce, “Dalilin da ba na sonsu, sa’ad da muna yara iyayemnıu kan rika hana tsuntsaye ba mu labarun barayi, wai don kada mu koyi dabarar sata. Ko da na ke ba da labari kada ka yi tsammani zuba su na ke yi tsuu, ban san abin da na ke yi ba. Kafin in ba da labari sai na auna wanda ko bayana ba za a zarge ni ba a kansa. Ko da ya ke dai an ce duniya ba a iya musu, tun da na ke ba mutane labari har yau ban taba ba da na mata ba, don tsoron yin mugun baki. Kuma ban da labarin Annabi Sulaimanu da na bayar sau daya, har yau ban ta6a bada labarin wani Annabi ba, ko da su ke duk ra’asan su ke a gare ni. Tsoron kada wadanda ba su sani ba su ji su ce sa6o na ke yi, shi ya hana ni takalar labarunsu, ko da ya ke sunfi kome dadi. In ko kana so ka ba da labarin 6arayi, sai ka ba da na zamanin jahiliyya, wadanda ko dabarun da su ke yi suna sata in an gaya wa mutanen yanzu da idonsu ya waye, sai su yi mamakin yadda mutanen da ke yarda a yaudare su da irin wadannan dabaru.”
Sarkin Sirika ya ce, “Wannan magana gaskiya ce.” Waziri yana duban Hazik tsurut, yana yi masa dariya.
Da Hazik ya ji haka sai ya ce, “Ai ko da ma ni ba irin wadanda ke bata halin mutane na ke so in yi ba.”
Waziri ya ce, “To, gaya mana labari guda na barayin lokacin jahiliyya mu ji, in da dadi nan gaba a fara, in ko ba dadi daga wannan a rufe.”
Hazik ya kada kai ya ce, “Hakanan ne.”
Labarin Sarkin Noma da 'Ya "Yansa
sami wata 'yar kafa ya 6alla da gudu, ku tara, ku tara, ya yı musu fintinkau, wani Dogari mai kili ya sake shi ya bi shi, ya sa doki ya banke shi. Ja'irin naka sai ya yi laya, aka nemehi qasa ko bisa, ya sulale yayi tafiyarsa yana haki, ko riga bai tsira da ita ba, daga shi sai bante da mayafin da ya kwanta da su. Dama dami ya fadi kan kaba, lokacin tafiyarsa gida ya yi, saboda haka ya sami ’yar sanda ya tasar wa garinsu. Ga shi nan tik ba sutura, ba ko abin sayen tuwo a hanya. Saboda haka gogan naka sai ya riqa fizge. in ya tarad da maciya sai ya tsaya, ya ce a sa mai abinci na taro ko na kwabo biyu. Da ya ci ya koshi sai yu tashi ya dauki sandarsa ya sa6a, zai wuce. In mai tuwo ta tambaye shi kudi sai ya zura a guje, ya ce, “Biyo ni ki karba!” Kama kama ya tsere. Haka ya yi ta yi har ya isa.
Sarakuna suka ce, “A, a, a! Ashe haka labarin barayi ke da dadin ji, Waziri ka hana a gaya mana su?”
Waziri ya ce, “Da ma akwai abin da ya fi labarin barayi dadi? Wadansu ne da ba su iya ba da su ba su ke fadin wadanda za su yiwu a bi a koyi sata. Kamar irin wannan daga farko ya yi kyau, amma daga baya ya so ya koma yadda ba mu so ba wajen satar jakan nan. Amma duk da haka ba laifi, ya yi dan dama.”
Hazik zai ci gaba da ba da labarin su Jimrau da Kosau, Alkalai suka ce, “Bari hakanan, Waziri 'kuma ya ba da wani sa’an nan gobe ka ci gaba.”
Hazik ya ce, ‘To, Waziri, gare ka. Ci gaba.” Waziri ya fara:
Da Muguwar Rawa Gwamma Kin Tashi
Sarki ya ce, “To, sau nawa na zo?”
Jakadiya ta ce, “Sau biyu ke nan mana ko? Yanzu ba ka zo ka karbi fam biyar ba? Watau yau fam shida ke nan fa ka karba da sule goma.”
Da jin haka Sarki ya san abin da ya auku, lalle wani ya yiwo irin shigarsa ya zo ya kar6i fam biyar. Ga shi ba wanda ya wuto su sa’ad da suna hira. Saboda haka ya san ba shakka ’yam bargansa ne. Amma da ya ke yana da wayo, ba ya son ya tona maganar, kada Jakadiya ta yi ta kwakwazo har barawon ya ji ya boye, sai ya yi murmushi ya ce, “In na karba sau goma, na ce ko nawa ne?” Ya wuce fuu, kamar yana fushi, ya yi waje. Ya ce a ransa, “Hakika wanda ya yi wannan aiki yanzu yana can kwance gabansa na faduwa. In dai cikin ’yam barga ne, bari in tafi inda su ke kwana in qidaya su, wanda na ga ba shi nan shi ne barawon. In ko duk suna nan, wanda na taba na ji gabansa na faduwa shi zan tuhunta gobe.”
Sai ya tasar wa barga, ya tarar da ’yam barga duk sun yi hululu, suna barci suna diban iska. To, ana ko duhu, saboda haka ya qidaya duhu-duhunsu da ya ke gani, ya ga duhu ashirin da biyar, iyakarsu kuwa ke nan. Sai ya bi su yana sa hannu a kirjunansu yana jin yadda gaban kowa ke yi, har ya kawo kan dam bargan nan da ya yi sata. Ashe da ma idonsa quri yana ji, ba ya barci, yana kuma kallon Sarki a sace. Ko da ya ga Sarki ya tinkaro wurinsa sai tsoro ya qara kama shi, ga tsoron abin da ya yi, ga tsoron Sarki ya nuho shi, watakila ko zai gane shi ne. Sai gabansa ya dauka dar, dar, dar. Da Sarki ya dafa kirjinsa ya ji haka, sai ya gane lalle shi dai ne barawon.
Sarki na tsammani barci ya ke yi, ya yi kokarin ya duba fuskarsa ya ga ko wane ne. To, ba farin wata, shi ko ba ya son kawo fitila, don kada ya ta da wata hatsaniya cikin dare. Saboda haka ya dauki almakashi ya yi masa ’yar hana-salla kyas a gaban goshi, yadda zai iya gane shi. Ya koma gida abinsa ya shiga.
Wücewarsa ke da wuya sai dam bargan nan ya tashi, ya sami almakashi, ya bi ’yan uwansa duk ya yi musu ki salla a goshi daidai da nasa. Da gari ya waye suka taru suna wanke ido, wani ya dubi fuskar dan’uwansa, ya fashe da dariya, ya ce, “Wane, har ka fara ki-salla? Daga nan muka faffara, kuturu ya ga mai kyasfi.”
Wancan gudan ya dube shi, ya ce, “Wace ki-salla? Kai dai da ke neman kafircewa, ai ga shi nan ka tsayar. In takalata ka yi don in nuna wa mutane ka kama hanya, to, sun gani.”
Sai wani kuma ya dubi wani, ya ce, “Ai ba ku kadai ba kuka tsai da ki-sallar, har da wane, ku dube shi, ku gani. ln wata jaraba ce Shaidan ya saukar muku da ita haka, sai mu ce Allah ya taimake ku. Mu dai muna tudun mun tsira.” Ya tofar da mugun yawu, tuf.
Ashe wani can kuma ya hango fuskarsa, sai ya ce, “ Kai da ka ke tofad da yawu na karya ba ka ga naka nan ba? Ko kuwa don an ce gwano ba ya jin warin jikinsa?”
Wannan ya tashi da fada, “lna ya ke? lna ya ke?“ Ya harare shi ya ce, “Af, to, ko kai fa? An ce wa mutanen Dumbulun su je aiki. Ba ka fadi, ashe kai ma ka bi tafarkinsu ne? Gaskiya ka ke fada.”
Saura suka dube shi, suka ga kuwa hakanan ne, sai suka ce, “A’aha! Yau lafiya?” Kowa ya shafa goshinsa sai ya ji dan askin sirit, suka yi ta tafa hannuwa.
Dam bargan nan ya ce, “Ba kowa, ma’askin dare ne, ba ku san aikin ja’iri ba.”
Saura suka ce, “I, gaskiyar ka, shi fa, shi ne fa."
Suna nan suna ta kakabin yadda ya bi su su ashirn duk ya yi musu abu ‹faya, sai ga Sarki ya fito, ya ce su yi holi. Suka yi, ba su san abin da ya arrala ba. Ya koma gabansu, fara dubawan nan da zai yi sai ya ga ki-salla a goshin na farko. Sai ya kama hannunsa, zai wuce da shi cikin gida ya je ya tuhunce shi, in ya ki fadın gaskiya ya yanka shi, sai ya kyalla ido ya hango wani kuma da goshi askakke. Ya juyo nan da nan ya duba da kyau, sai ya ga ashe dukansu kowa na da ki-salla a goshi. Abin ya ba shi mamaki, har ya yi murmushi, don ya gane abin da ya faru. Zai yi magana sai ya ga ba shi da amfani ya ta da hankalinsa da hankalin barorinsa a banza, ba kuwa zai gane barawon ba. Ya ga tun da al’amarin ya ke haka, masu karin magana kuwa sun ce da muguwar rawa gwamma kin tashi, sai ya dubi ’yan, barga, ya ce, “Wanda ya yi abin da ya sa na holanta ku anan ya san kansa, ya kuma san abin da ya yi. To, ya san da sani ya yi daron yanka. Allah ya taimake shi, amma ya sani fa, in ya kuskura ya kara yin wannan kuru, asirinsa na tonuwa. Ba kullum a ke kwana a gado ba. Shi ke nan, ku tafi.”
Yam barga suka watse suna tambayar juna, ba wanda ya san abin da ya faru, balle su gane jawabin Sarki. Shi kuwa wannan dam bargan ko da ya ke ya sani da shi ake yi, ba damar ya furta ya jawo wa kansa. Ya ma furta ai yana so, ya ga aiki da cikawa. Gidan maqi gudi ai da kara a kan nuna.
Hazik ya ce, ‘Ai ga shi kai ma labarin barayin ka bayar. In ma da wanda ke yiwuwa a kwaikwaya, wannan naka ai ya fi ko wanne sauki.”
Waziri zai yi magana. Alkalai suka ga in sun kyale su suka fara gardama, har magar'ba ta yi ba a tashi ba. Sai suka ce, “To, ya isa hakanan, an yi kiran salla.” Duk mutanen suka watse.
Magariba na yi, Waziri ya sa aka yi toye-toye aka kai wa Hazik, ya ce watakila ya gaji da wahalar tahowa kullum.
Kashegari kuma da azahar aka sake cika bakin aiki. Hazifk ya haye bisa wani dan tebur, ya shiga sana’a. Zai ci gaba a da labarin da ya fara na ’ya’yan Sarkin noma da suka fita neman arziki. Jiya ya ba da na Nomau, yau kuwa zai ba da na Jimrau. Sai ya kama:
Comments
Post a Comment